Hukumar Kula da Harkokin Hako Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ta bayyana cewa ana gudanar da fiye da ayyuka 1,100 a ƙauyukan da ke karɓar ayyukan kamfanonin mai a yankin Neja Delta, ƙarƙashin tsarin Host Communities Development Trust (HCDT) da Dokar Petroleum Industry Act (PIA) ta tanada.
Mataimakin Daraktan Sashen Harkokin Ci gaban Ƙauyukan Masu Masaukin Mai na NUPRC, Kingsley Ehiaguina, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da Kwamitin Amintattu (Board of Trustees) na PML 66 Host Communities Development Trust wanda kamfanin Ingentia Energies Limited ya kafa a birnin Fatakwal na Jihar Rivers.
Ya ce tun bayan fara aiwatar da tsarin HCDT, an yi rajistar trust guda 163, yayin da aka tura biliyoyin naira cikin asusun su domin aiwatar da ayyukan ci gaba.
A cewarsa, an riga an kammala fiye da ayyuka 200, yayin da sama da ayyuka 1,100 ke ci gaba da gudana a sassa daban-daban na yankin Neja Delta.
Ehiaguina ya yabawa kamfanin Ingentia Energies bisa yadda yake bin tanade-tanaden Dokar PIA, yana mai tabbatar da cewa NUPRC za ta tabbatar kamfanoni suna biyan kaso 3% na kuɗin gudanar da aiki (OPEX) da doka ta wajabta domin ci gaban al’ummomin da suke aiki a cikinsu.
Shi ma Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Kamfanin Ingentia Energies Limited, Charles Odita, ya ce ƙaddamar da wannan trust zai kawo gagarumin sauyi wajen bunƙasa rayuwar al’ummomin da kamfanin ke aiki tare da su.
Ya bayyana cewa al’ummomin ne za su kasance masu yanke shawarar irin ayyukan ci gaba da suke buƙata bayan kamfanin ya ware kuɗaɗen da doka ta tanada.
A nasa jawabin, Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Masarautu da Harkokin Al’umma ta Jihar Rivers, Patrick Ndukwe, ya buƙaci kwamitin ya tabbatar ayyukan da za su zaɓa sun yi daidai da manufofin ci gaban gwamnatin jihar, musamman a fannoni kamar hanyoyi, ilimi, lafiya, noma da bunƙasa ƙauyuka.
Tun da farko, mai ba kamfanin Ingentia Energies shawara, Godwin Minimah, ya ce ƙaddamar da kwamitin wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kamfanin da al’ummomin da yake aiki a cikinsu.
