Shugabar Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Abuja, Kwamared Grace Ike, ta bukaci ‘yan jarida su kasance masu kare dimokuradiyya ta hanyar tabbatar da gaskiya da kaucewa yada labaran karya a kasar nan.
Ta bayyana hakan ne yayin bude taron makon manema labarai da bayar da kyaututtuka na NUJ-FCT da aka gudanar a Transcorp Hilton da ke Abuja.
Grace Ike ta ce yada bayanan karya da karkatar da gaskiya na kara zama barazana ga zaman lafiya da dimokuradiyya, musamman a lokacin da kafafen sada zumunta ke sa bayanai yaduwa cikin sauri.
“A matsayinmu na ‘yan jarida, dole ne mu tabbatar da sahihancin bayanai tare da bayar da rahotanni masu gaskiya da adalci,” in ji ta.
Ta kara da cewa aikin jarida na taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun jama’a da kuma tabbatar da dorewar dimokuradiyya a Najeriya.
Shugabar ta yabawa wadanda aka karrama a wajen taron bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunkasa aikin jarida mai inganci.
Haka kuma ta godewa kamfanoni da kungiyoyi da suka tallafa wajen gudanar da taron, tana mai cewa hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da masu ruwa da tsaki na taimakawa wajen karfafa dimokuradiyya.
A karshe, ta bukaci ‘yan jarida su ci gaba da nuna jarumtaka da rikon gaskiya wajen gudanar da ayyukansu domin makomar dimokuradiyyar Na0jeriya.
