Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da sauya mukaman wasu kwamishinoni a gwamnatinsa domin inganta gudanar da ayyukan gwamnati a jihar.
A karkashin sabon sauyin, an mayar da Sali Idris daga Ma’aikatar Kula da Dabbobi zuwa Ma’aikatar Noma, yayin da aka tura Farfesa David Jatau daga Ma’aikatar Noma zuwa Ma’aikatar Kula da Dabbobi.
Haka kuma, an sauya Muhammad Chubado daga Ma’aikatar Raya Makamashi zuwa Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jin Kai.
A wani mataki na wucin gadi, Kwamishinan Harkokin Musamman, Usman Lamurde, zai kula da Ma’aikatar Kula da Dabbobi har sai Farfesa Jatau ya dawo daga hutun rashin lafiya da yake yi.
Gwamna Fintiri ya kuma sanar da tura sabon kwamishinan da aka nada, Leader Leneke, zuwa Ma’aikatar Yada Labarai da Dabarun Gwamnati bayan murabus din James Iliya.
Iliya ya yi murabus daga mukaminsa ne domin neman tikitin tsayawa takara na jam’iyyarsa domin wakiltar mazabar Demsa a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa.
