Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, bayan kammala zaben fidda gwani na sanatoci na jam’iyyar APC a jihar.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, Keyamo ya taya ‘yan takarar sanatocin APC murna tare da yabawa yadda aka gudanar da zaben a fadin jihar.
“Na yi matukar farin ciki da taya Sanata Ifeanyi Okowa (Delta North), Sanata Ede Dafinone (Delta Central), da Sanata Joel-Onowapo Thomas (Delta South) murnar samun nasara mai girma,” in ji shi.
Ya bayyana cewa nasarar tasu ta dace da irin goyon bayan da suka samu daga ‘ya’yan jam’iyya.
Keyamo ya ce zaben ya samu halartar dimbin magoya bayan APC a matakin mazabu, yana mai cewa tsarin ya nuna sahihin dimokuradiyya a cikin jam’iyyar.
“Zaben fidda gwanin da aka gudanar ya samu halartar hakikanin ‘ya’yan APC a matakin mazabu, kuma an gudanar da shi cikin adalci da gaskiya,” ya bayyana.
A cewarsa, wannan shi ne mafi ingancin zaben fidda gwani da APC ta taba gudanarwa a jihar Delta tun bayan kafuwar jam’iyyar.
Ya kuma bukaci wadanda suka sha kaye da su rungumi sakamakon zaben tare da hada kai domin ci gaban jam’iyyar kafin babban zaben 2027.
“Yanzu lokaci ne na sulhu da hadin kai. Ina rokon wadanda suka sha kaye da su karbi sakamakon cikin mutunci tare da mara wa wadanda suka yi nasara baya,” in ji Keyamo.
Haka kuma ya bukaci wadanda suka yi nasara da su kasance masu yafiya tare da hada kan dukkan ‘ya’yan jam’iyyar.
Ministan ya yabawa Gwamna Sheriff Oborevwori bisa abin da ya kira shugabanci nagari da hada kai a jihar Delta.
Sannan ya jinjinawa Shugaba Bola Tinubu bisa tabbatar da dimokuradiyya a cikin APC da kuma bai wa kowa damar fafatawa cikin adalci.
“Ana ganin wannan a matsayin daya daga cikin mafi ingancin zabukan cikin gida da APC ta gudanar a fadin kasa,” in ji shi.
A karshe, Keyamo ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar su ci gaba da aiki tukuru tare da nuna kwarin gwiwa gabanin zaben 2027, yana mai cewa, “Nasara tana gaba.”
