Ƙasar Finland na shirin ƙaddamar da sabbin dokoki masu tsauri ga ɗaliban ƙasashen waje a ƙarƙashin wani sabon tsarin gyaran dokokin shige da fice da gwamnati ke shiryawa.
Rahotanni sun bayyana cewa sabbin dokokin za su haɗa da ƙarin sharuddan harshe, tsauraran binciken kuɗaɗen ɗalibai, da kuma jinkirta damar haɗa iyali ga masu zuwa karatu.
A cewar rahoton Economic Times, ma’aikatar harkokin tattalin arziki da ayyukan yi ta Finland ta fitar da kudirin ne a ranar 18 ga Mayu domin karɓar ra’ayoyin jama’a kafin ranar 29 ga Yuni.
Idan aka amince da kudirin, za a miƙa shi gaban majalisa a zaman bazarar shekarar 2026, yayin da ake sa ran fara aiwatar da shi daga shekarar 2027.
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka tsara shi ne hana ɗaliban ƙasashen waje zuwa da iyalansu tare lokacin da suka isa Finland.
Sabon tsarin ya nuna cewa dole ne ɗalibi ya shafe akalla shekara guda a Finland kafin iyalansa su samu damar neman bizar zuwa ƙasar.
Mahukunta sun ce an tsara hakan ne domin tabbatar da cewa ɗalibai suna da ƙarfin tattalin arziki da zai hana su shiga matsin rayuwa ko fadawa tarkon masu yaudarar neman gurbin karatu.
Ministan Ayyukan Yi, Matias Marttinen, ya ce sabbin dokokin na da nufin daidaita bukatar ƙwararrun ma’aikata da kuma kula da dorewar tsarin shige da fice.
Ya ce: “Kasuwar aikin Finland na bukatar ƙwarewar ɗaliban ƙasashen waje a gaba, amma dole ne a tabbatar cewa tsarin yana dorewa kuma ba ya jefa mutane cikin matsala.”
Sabbin dokokin kuma za su kafa mafi ƙarancin kuɗin shiga da ɗalibai za su nuna kafin samun izinin zama, maimakon tsarin shawarwari da ake amfani da shi yanzu.
Haka kuma, gwamnati na shirin kafa gwajin ƙwarewar harshe kafin shiga ƙasar, inda ɗaliban da ba su kai matakin da ake buƙata ba za a iya hana su izinin zama.
Mahukunta sun bayyana cewa wasu ɗalibai kan shiga ƙasar ba tare da isasshen ilimin harshe ba, abin da ke kawo musu matsala wajen gudanar da karatunsu cikin nasara.
Sabbin sauye-sauyen na daga cikin matakan da Finland ke ɗauka tun daga shekarar 2023 domin ƙarfafa tsarin shige da fice da inganta yadda baki ke shiga rayuwa da karatu a ƙasar.
