Jam’iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Anambra ta kammala zaben fidda gwani domin shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027, inda ta fitar da ‘yan takara domin kujerun Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Awka ranar Alhamis, shugaban jam’iyyar a jihar, Peter Okoye, ya bayyana cewa an gudanar da zaben ne ta hanyar tsarin Option A4, wanda ya samu halartar mambobi, wakilai, masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki.
Okoye ya ce zaben ya gudana cikin lumana da gaskiya, tare da nuna jajircewar jam’iyyar wajen tabbatar da dimokuradiyya ta cikin gida da kuma bai wa talakawa damar shiga harkokin siyasa.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan takarar da aka fitar cewa shugabanci da mambobin jam’iyyar za su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasararsu a babban zaben 2027.
A cewarsa, an amince da ‘yan takarar ne ta hanyar kuri’ar rinjaye a wani taron musamman na tantance ‘yan takara da aka gudanar bisa tanadin kundin tsarin mulkin Labour Party, Dokar Zabe ta 2026 da kuma ka’idojin zaben cikin gida na jam’iyyar.
Okoye ya ce:
“Muna farin ciki da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da gaskiya, lamarin da ya kara nuna kudirin jam’iyyar wajen tabbatar da dimokuradiyya ta cikin gida da kuma bai wa mambobi damar yanke hukunci kai tsaye.
“An gudanar da zaben ne ta tsarin Option A4, kuma ya samu gagarumar halartar mambobi, wakilai, masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki.”
Jam’iyyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa sakamakon zaben fidda gwanin zai kara hada kan mambobinta tare da taimakawa wajen samun nasara a zaben 2027.
