Dan wasan gaba na Jamus kuma tauraron Arsenal, Kai Havertz, ya bayyana cewa yawan hazikan ‘yan hari da kasar ke da su zai kasance babban karfi ga tawagar kafin fara Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026.
Havertz ya ce gasa mai zafi tsakanin ‘yan wasa domin samun gurbi a cikin tawagar kocin Julian Nagelsmann abu ne mai kyau, yana mai jaddada cewa zurfin tawagar zai taimaka wa Jamus sosai a gasar da za a gudanar a Arewacin Amurka.
Jamus na da manyan ‘yan wasa masu kai hari irin su Florian Wirtz, Jamal Musiala da kuma dan wasan Stuttgart, Deniz Undav, wanda ke ci gaba da nuna bajinta a kulob dinsa da kuma tawagar kasa.
Duk da tsananin gasa wajen samun gurbin fara wasa, Havertz ya ce ‘yan wasan sun fi mayar da hankali kan nasarar kungiyar baki daya maimakon burin kashin kai.
“Munada zabuka da dama a bangaren kai hari. Wannan matsala ce mai dadi ga kowace kungiya. Ya fi kyau ka samu kwararrun ‘yan wasa da yawa fiye da ka rasa su,” in ji Havertz.
Tsohon dan wasan Chelsea din ya kuma bayyana cewa tawagar Jamus na da ‘yan wasa masu iya taka rawar gani a wurare daban-daban a filin wasa.
“Akwai bambancin kwarewa a cikin tawagar. Muna bukatar kowane dan wasa, kuma da yawa daga cikinsu na iya taka leda a matsayi fiye da daya,” ya kara da cewa.
Da aka tambaye shi ko yana jin tsoron gasa daga Deniz Undav wanda ke cikin kyakkyawan yanayi, Havertz ya yi watsi da wannan tunanin.
“Kididdigarsa tana magana da kanta. A cikin tawagar kasa yana da muhimmanci matuka. Mu ‘yan wasa mun san hakan sosai.
“Babu wanda ke tsoron wani. Dole ne mu yi aiki tare a matsayin kungiya kuma kowa zai kasance da muhimmanci,” in ji shi.
Kai Havertz na ci gaba da kasancewa daya daga cikin fitattun ‘yan wasan Jamus saboda iya taka leda a wurare daban-daban da kuma fahimtarsa ta dabarun wasa, yayin da kasar ke shirin tunkarar Gasar Kofin Duniya ta 2026.
