Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya gargadi matasan Najeriya da su guji fadawa tarkon rarrabuwar kawuna ta fuskar kabila da addini, yana mai cewa hakan na iya zama wata hanya da wasu ke amfani da ita wajen raunana hadin kan kasa.
Obi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da ake ci gaba da muhawara a kafafen sada zumunta kan Fasto Enoch Adeboye, Babban Mai Kula da Cocin RCCG, dangane da matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.
Ya ce darasin da aka koya daga zaben 2023, musamman a jihar Legas, shi ne yadda ake karkatar da hankalin jama’a daga batutuwan ci gaba da shugabanci zuwa rikice-rikicen kabila da addini.
A cewarsa, wasu ‘yan siyasa kan yi amfani da irin wadannan rarrabuwar kawuna idan suka kasa fafatawa da manufofi, ayyuka da hangen nesa.
Obi ya kare Fasto Adeboye, yana mai bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagororin addini da suka dade suna wa’azin zaman lafiya, hadin kai da sulhu a Najeriya.
Ya ce bai dace a dora wa mutum mai shekaru 84 nauyin da ya kamata matasa su dauka wajen fafutukar kawo canji a kasar ba.
“Gina Najeriya mai kyau ya rataya ne a wuyan matasa. Su ne ya kamata su jagoranci tattaunawa, gyare-gyare da kuma sauye-sauyen da kasar ke bukata,” in ji Obi.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su rika tantance bayanai kafin su yarda da su, tare da kauce wa duk wani yunkuri na haddasa rabuwar kai.
Obi ya jaddada cewa Najeriya za ta samu ci gaba ne idan al’umma suka zabi hadin kai da zaman lafiya maimakon kiyayya da son zuciya.
