Kungiyoyin rajin kare haƙƙin mata sun ƙaddamar da gangamin “Women for Women” a Kaduna domin ƙarfafa goyon bayan ‘yan takarar mata da suka samu tikitin jam’iyyunsu gabanin zaɓen 2027.
Labarin:
Kungiyoyin rajin kare haƙƙin mata a Najeriya sun fara wani babban gangamin wayar da kai mai suna “Women for Women” domin ƙarfafa goyon baya ga ‘yan takarar mata da suka samu tikitin jam’iyyunsu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
An ƙaddamar da shirin ne a birnin Kaduna yayin wani taro da aka shirya domin tattauna hanyoyin ƙara yawan shigar mata cikin harkokin shugabanci da siyasa.
Shugabar reshen mata ta ƙungiyar Peace Revival and Reconciliation Foundation of Nigeria, Hajiya Ramatu Tijjani, ta bayyana cewa manufar gangamin ita ce haɗa kan mata domin tallafa wa juna ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Ta ce fitowar mata da suka samu tikitin takara daga jam’iyyunsu wata muhimmiyar dama ce da ya kamata a yi amfani da ita wajen ƙarfafa wakilcin mata a gwamnati.
“Idan mata suka haɗa kai suka mara wa juna baya a zaɓe, za a samu ƙarin mata da za su yi nasara tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa,” in ji ta.
Ramatu ta ƙara da cewa gangamin zai bazu zuwa sassan ƙasar domin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a da kuma ƙarfafa mata su fito su goyi bayan ‘yan takarar mata.
A nata jawabin, shugabar Jam’iyyar Matan Arewa, Hajiya Rabi Saulawa, ta nuna damuwa kan ƙarancin mata da suka samu tikitin takara a zabukan fidda gwani da aka gudanar.
Ta yi kira ga mata da su ƙara nuna haɗin kai da goyon baya ga juna domin samun wakilci mai ƙarfi a matakan gwamnati daban-daban.
Jagororin matan sun jaddada cewa ƙarin shigar mata cikin siyasa zai taimaka wajen magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da kuma ƙarancin damar ilimi, tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya da cigaban al’umma.
Sun kuma bayyana cewa ci gaba da wayar da kai, tattara masu kaɗa ƙuri’a da kuma samun goyon bayan hukumomi na daga cikin muhimman matakan da za su taimaka wajen inganta damar mata a zaɓen shekarar 2027.
