Gwamnatin Jihar Anambra State ta yi alkawarin tabbatar da adalci ga wata yarinya mai shekara 16 da aka yi wa fyade ta hanyar taro da wasu maza takwas, ciki har da mai kula da ita, a garin Nawfia da ke Karamar Hukumar Njikoka.
Kwamishiniyar Harkokin Mata da Jin Dadin Al’umma ta jihar, Esther Onyekesi, ta bayyana hakan yayin da aka kawo yarinyar ofishinta da ke Awka.
Kwamishiniyar, cikin damuwa da alhini, ta ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa an hukunta duk wadanda ke da hannu a wannan mummunan laifi domin ya zama izina ga sauran mutane.
Rahoton likitoci ya tabbatar da cewa yarinyar na dauke da ciki mai wata biyu sakamakon cin zarafin da aka dade ana yi mata.
An ce wani limamin cocin Katolika daga Nawfia ne ya kai karar lamarin bayan ya samu labarin abin da ke faruwa.
Onyekesi ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da wannan aika-aika, tana mai jaddada cewa wajibi ne a kare yara mata da mata daga cin zarafi maimakon anfani da raunin da suke ciki.
A bayaninta, yarinyar ta ce mai kula da ita yana lalata da ita kusan kowace dare, sannan daga baya wasu maza suka shiga cikin cin zarafin.
Ta ce wani mutum mai tausayi ne ya taimaka wajen ceto ta daga wannan hali a makon da ya gabata, lamarin da ya kai ga kama wasu daga cikin wadanda ake zargi.
Yarinyar ta kuma bayyana cewa matar mai kula da ita na fama da cutar shanyewar jiki, abin da ya hana ta iya dakile cin zarafin.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar ‘yan sanda ta Nawfia ta kama mutane biyu daga cikin wadanda ake zargi, yayin da sauran shida suka tsere kuma ake neman su.
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Nawfia.
Lamarin ya sake tayar da hankulan jama’a kan bukatar kara tsaurara matakan kare yara daga cin zarafi da kuma tabbatar da hukunta masu aikata irin wadannan laifuka.
