Majalisar Dokokin ƙasar Senegal ta zaɓi tsohon Firaminista Ousmane Sonko a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin ƙasar ranar Talata.
An zaɓi Sonko ne bayan an dawo da shi cikin majalisar a wani zama da ‘yan adawa suka kaurace wa halarta.
Sonko shi ne kaɗai ɗan takarar da ya tsaya neman kujerar, inda ya samu kuri’u 132, ba tare da wani ɗan majalisa ya ƙi zaɓensa ba, yayin da mutum guda ya kaurace wa kaɗa kuri’a.
Mai jagorantar zaman majalisar, Ismael Diallo, ya tabbatar da sakamakon zaɓen.
Majalisar dokokin Senegal tana da kujeru 165 gaba ɗaya.
