An tsaurara matakan tsaro a hanyoyin shiga Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja a ranar Alhamis, yayin da jami’an ‘yan sanda masu yaki da tarzoma suka mamaye manyan kofar shiga fadar.
Rahotanni sun nuna cewa karin jami’an tsaron ya biyo bayan shirin da dan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi na jagorantar masu zanga-zanga zuwa Aso Rock domin neman a ceto daliban makarantu da malamansu da aka sace a jihohin Oyo da Borno.
An ga jami’an ‘yan sanda dauke da kayan kariya na musamman suna tsaye a kofar shiga fadar, yayin da aka takaita shiga wurin ga masu katin shaidar Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa kadai.
Sowore ya bayyana cewa zanga-zangar za ta fara ne daga Eagle Square da ke Abuja, inda masu zanga-zangar za su nufi Aso Rock karkashin taken #OccupyAsoRock, domin matsa wa gwamnatin tarayya lamba ta tabbatar da sakin yaran da aka sace.
Ya ce manufar zanga-zangar ita ce tunatar da gwamnati nauyin da ke kanta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai cewa idan ba a samu nasarar ceto daliban ba, shugaban kasa ya kamata ya dauki alhakin gazawar da aka yi wajen samar da tsaro.
Sowore ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su mayar da hankali wajen kare makarantu da dalibai maimakon dakile zanga-zangar lumana.
Lamarin ya shafi sace dalibai da malamai kusan 46 daga makarantu uku a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, da kuma wasu dalibai 42 da aka sace daga wata makaranta a Askira-Uba ta jihar Borno a ranar 15 ga Mayu, 2026.
A martanin gwamnati, Shugaba Bola Tinubu ya tura wata babbar tawaga karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, tare da amincewa da daukar sabbin masu gadin dazuka 1,000 da kuma kafa rundunar musamman domin aikin ceto wadanda aka sace.
Haka kuma, Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) ta shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani a jihar Oyo domin nuna damuwa kan matsalar tsaro da kuma neman a gaggauta ceto daliban da malamansu.
Masu sa ido kan harkokin tsaro na ganin cewa yadda lamarin ke gudana zai ci gaba da jan hankalin jama’a, musamman yayin da ake ci gaba da matsin lamba ga gwamnati ta kawo karshen matsalar garkuwa da mutane a fadin kasar.
