Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ta mika kayan aiki ga Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) da kuma Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN) domin inganta ayyukan su a yankin.
A cewar wakilin NEDC, Alkali, za a raba keken ɗaukar kaya (trolleys) 130 zuwa jihohi shida na Arewa maso Gabas domin sauƙaƙa harkokin sufuri a filayen jiragen sama.
Ya ce FAAN na daga cikin muhimman hukumomin da aka yi la’akari da su saboda kalubalen da ake fuskanta a filayen jiragen sama.
A cewarsa, an fara ne da kayan asali kamar trolleys saboda karancin su, kafin a shiga wasu manyan matakai na ci gaba a gaba.
An raba trolleys din kamar haka:
Adamawa – 20
Bauchi – 20
Borno – 30
Gombe – 20
Taraba – 20
Yobe – 20
Haka kuma, an mika kayan aikin rediyo ga FRCN wanda ya hada da na’urar watsa shirye-shirye (5KW transmitter), eriya, kwamfutoci, microphones, consoles, fitilu da sauran kayan studio.
Daraktan Janar na FRCN, Muhammad Bulama, ya ce wannan tallafi zai taimaka wajen kara yawan lokutan watsa shirye-shirye a yankin Arewa maso Gabas, yana mai cewa tashoshin na iya watsa shirye-shirye na tsawon sa’o’i 12 zuwa 15 a rana.
A nasa bangaren, wakiliyar FAAN a filin jirgin Muhammadu Buhari da ke Maiduguri, Fatima Aliyu, ta ce trolleys din za su taimaka wajen saukaka daukar kayayyakin fasinjoji a filayen jiragen sama na yankin.
