Dan wasan bayan gefen dama na Blackburn Rovers, Ryan Alebiosu, ya bayyana cewa fara buga wasa a kungiyar Super Eagles na Najeriya na daga cikin manyan abubuwan da suka fi birge shi a rayuwar kwallon kafarsa.
Dan wasan mai shekaru 23 ya samu damar buga wasan sa na farko a matakin manya ne a wasan da Najeriya ta doke Uganda da ci 3-1 a gasar Africa Cup of Nations ta 2025 da aka gudanar a Morocco.
A wata hira da ya yi da Rovers TV, Alebiosu ya ce burinsa shi ne ya ci gaba da wakiltar Najeriya, yana mai cewa kwarewar ta kara masa kwarin gwiwa da kuma burin ci gaba.
Ya ce: “Na dauki hakan a matsayin kari ne kawai. Lokacin da na sanya hannu, ban yi tunanin samun kiran kasa nan kusa ba. Amma da ya faru, kamar mafarki ne ya zama gaskiya.”
“Wasan kasa da samun kira daga Najeriya yana daya daga cikin manyan abubuwan alfahari a rayuwata. Ya kara min karsashi sosai,” in ji shi.
Ya kara da cewa kiran da aka masa zuwa Super Eagles ya taimaka wajen kara masa kwarin gwiwa a fili da kuma tunanin cewa akwai damar da za ta iya kara budewa a gaba.
“Abin ya sa na kara himma sosai. Ya nuna min cewa akwai abubuwa da dama da za su iya faruwa, kuma ina da abubuwa da zan kara kawowa,” in ji shi.
Alebiosu ya ce samun damar wakiltar Najeriya yana da matukar muhimmanci gare shi, yana mai cewa hakan ya kara masa buri da kuzari wajen ci gaba da inganta wasansa a matakin kulob da na kasa.
