Tauraruwar fina-finan Nollywood, Shine Rosman, ta bayyana irin wahalhalun da ta fuskanta a rayuwa, inda ta ce mutane sun rika hasashen cewa za ta zama karuwa bayan rasuwar mahaifinta tana da shekaru 16.
Shine Rosman ta bayyana hakan ne a wata hira da shahararren mai gabatar da shirye-shirye, Chude Jideonwo, inda ta ce mutuwar mahaifinta ta yi mata matukar raɗaɗi tare da jefa ta cikin bakin ciki mai tsanani har ma ta kai ga tunanin kashe kanta.
Ta ce a lokacin da take cikin bakin ciki da kuma matsin tattalin arziki da ya biyo baya, wasu mutane sun yi mata kallon mara kyau, suna cewa za ta dauki ciki ba tare da aure ba saboda rashin uba.
“Bayan na rasa mahaifina ina da shekara 16, mutane da yawa sun rika cewa zan zama karuwa kuma zan dauki ciki ba tare da aure ba. Bakin ciki na iya kai mutum matakin tunanin kashe kai saboda yana daga cikin mawuyacin abu da mutum ke fuskanta,” in ji ta.
Duk da haka, ta bayyana cewa ta yi amfani da kalaman mutane da kuma wahalhalun rayuwa wajen kara karfi da himma har ta samu nasara a rayuwarta.
Ta kara da cewa wahalar da ta sha tun tana karama ce ta taimaka mata wajen gina ƙwazo da jajircewa a harkar aiki, inda ta ce da ba ta taso a irin wannan yanayi ba, wataƙila ba za ta zama mai himma kamar yanzu ba.
