Yayin da ya rage kwanaki uku kacal a fara Gasar Commonwealth ta 2026, tawagar Team Nigeria ta fara barin sansanin atisayenta da ke Aberdeen zuwa birnin Glasgow, inda za a gudanar da gasar.
Kashi na farko na ‘yan wasa da jami’an tawagar zai tashi zuwa Glasgow, yayin da sauran mambobin tawagar za su isa Games Village kafin fara wasannin.
Team Nigeria ta shafe makonni tana atisaye da shirin tunkarar gasar a Aberdeen, inda Hukumar Kula da Wasanni ta Kasa (NSC) ta samar musu da cikakken tallafin horo, lafiya da walwala domin tabbatar da sun isa gasar cikin ƙoshin lafiya da cikakken shiri.
Najeriya za ta fafata a wasanni daban-daban, kuma ana sa ran ‘yan wasan za su yi kokari wajen lashe lambobin yabo bayan kyakkyawan rawar da suka nuna a gasannin nahiyar Afirka da na duniya.
Za a gudanar da Gasar Commonwealth ta Glasgow 2026 daga 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agusta, inda kusan ‘yan wasa 3,000 daga ƙasashe da yankuna 74 za su fafata a wasanni 11 domin neman lambobin zinariya 215.
Hukumar NSC ta bayyana kwarin gwiwa cewa Team Nigeria na da cikakken shiri kuma za ta wakilci ƙasar cikin mutunci tare da fafutukar lashe lambobin yabo a gasar.
