Fitaccen ɗan wasan barkwanci, jarumi kuma mai ƙirƙirar abun ciki a Najeriya, Michael Sani Amanesi, wanda aka fi sani da MC Lively, ya sanar da cewa zai angwance da amaryarsa, Dumebi James.
MC Lively ya bayyana hakan ne ta shafukansa na sada zumunta, inda ya wallafa hotunan gab daurin aurensu (pre-wedding photos), lamarin da ya jawo taya murna daga masoya da abokan aikinsa.
MC Lively ya yi fice ne ta hanyar gajerun bidiyoyin barkwanci da yake fitowa a matsayin “Barrister Mike”, inda yake nuna kalubalen rashin aikin yi da sauran matsalolin rayuwar yau da kullum a Najeriya.
Kafin ya shiga harkar nishaɗi, MC Lively ya kammala karatun lauya a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), sannan aka kira shi zuwa ƙungiyar lauyoyin Najeriya (Nigerian Bar) a shekarar 2016.
Baya ga barkwanci, ya taka rawa a fina-finan Nollywood da dama, ciki har da Fate of Alakada, Seven and a Half Dates, da Breaded Life.
Tun bayan sanar da shirin auren nasa, dubban masoya, abokan sana’a da masu fatan alheri sun cika shafukansa na sada zumunta da saƙonnin taya murna tare da yi masa fatan alheri a sabon babin rayuwarsa
