Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya bayyana cewa jita-jitar da aka rika yadawa kan rashin haihuwarsa ta kusa hana shi samun kujerar sarautar gargajiya.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da baki a fadarsa yayin bikin murnar zuwan tagwaye da matarsa ta farko, Olori Mariam, ta haifa kwanan nan.
Oba Ogunwusi ya ce kafin zuwan tagwayen, ya fuskanci tsananin matsin lamba da bincike daga jama’a, musamman ganin wasu daga cikin matansa sun bar fadar ba tare da samun ‘ya’ya ba.
Ya ce wannan ya sa wasu ke yada jita-jita cewa ya yi asarar haihuwa saboda dukiya da matsayi da yake da shi.
“Sun ce na yi amfani da haihuwata saboda dukiya, shi ne dalilin da ya sa wasu matan nawa suka tafi ba tare da haifa mini ‘ya’ya ba,” in ji sarkin.
Ya kara da cewa ya shafe shekaru takwas a kan karaga yana fuskantar wannan matsala, wadda ya ce ta zama jarabawa a gare shi, har sai da ya koma addu’a sosai kafin samun sauki.
Sai dai bayan kalamansa sun fito, mutane a kafafen sada zumunta sun rika muhawara, inda wasu ke tambayar yadda maganar ta dace da bayanan cewa yana da ‘ya’ya, ciki har da dan da ya samu a lokacin da Olori Naomi ke fada.
