Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta sanar cewa kamfanin jiragen sama na Ibom Air zai kaddamar da jirgin farko na ƙasa da ƙasa daga Uyo zuwa Accra, Ghana, a ranar Asabar 2 ga Mayu, 2026.
Wannan sanarwa ta fito ne daga Gwamna Umo Eno, wanda ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Shugaban ƙasa kan haɓaka filin jirgin sama na Victor Attah zuwa matakin ƙasa da ƙasa.
Jirgin zai tashi daga Victor Attah International Airport da ke Uyo zuwa Kotoka International Airport a Accra, inda kuma za a yi jirgin dawowa ranar 3 ga Mayu, 2026.
Gwamna Eno ya bayyana wannan ci gaban a matsayin babban mataki wajen inganta harkokin zirga-zirgar jiragen sama, yawon buɗe ido, kasuwanci da kuma zuba jari a jihar.
Ya kuma gode wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, saboda goyon bayan da suka bayar wajen cimma wannan buri.
Haka kuma, an ce kaddamarwar na zuwa ne bayan an tabbatar da cewa filin jirgin ya kai matakin da ya dace domin fara zirga-zirgar ƙasashen waje, bayan binciken da aka gudanar a ƙarshen 2025.
Hukumomi sun ce wannan mataki zai ƙara buɗe ƙofofin tattalin arziki ga Akwa Ibom, tare da ƙarfafa matsayinta a harkar sufuri da kasuwanci a yankin.
