Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta bayyana cewa ta fara daidaita tsare-tsare domin cimma burin samar da ganga miliyan 3 na mai a kowace rana, tare da sake fasalin kasuwar wutar lantarki domin jawo masu zuba jari da inganta tattalin arziki.
Wannan shiri na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da ƙarancin samar da mai ƙasa da ganga miliyan 1.5 a rana, tare da matsalolin wutar lantarki da ke shafar masana’antu da gidaje.
Wata tattaunawa da aka gudanar a ranar Litinin tsakanin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar makamashi, Olu Verheijen, da ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ta mayar da hankali kan yadda za a haɗa manufofin haraji da na sassa daban-daban domin jawo jari.
A tattaunawar, an mayar da hankali kan aikin ofishin Energy Reforms Nigeria domin tallafa wa shirin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙara yawan fitar da mai zuwa ganga miliyan 3 a rana.
Haka kuma, an tattauna kan yadda za a sake tsara tsarin kasuwar wutar lantarki domin ta zama mai inganci, mai jan hankalin masu zuba jari, da kuma samar da jarin dogon lokaci mai dorewa.
A halin yanzu, Najeriya na samar da ƙasa da megawatt 5,000 na wutar lantarki, alhali bukatar ƙasa ta haura megawatt 40,000, abin da ke ci gaba da hana ci gaban masana’antu.
Duk da muhimmancin shirin, ba a bayyana takamaiman lokacin aiwatarwa ko cikakken sakamakon manufofin da aka tattauna ba.
