Akalla mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu mutane da dama suka jikkata a wani harin bindiga da ya faru a wata makaranta ta sakandare a lardin Kahramanmaras da ke kudancin Turkiyya a ranar Laraba.
Gwamnan yankin, Mukerrem Unluer, ya tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da rahotanni suka ce akalla mutane shida sun samu raunuka a harin.
Shaidu sun bayyana cewa harbin bindigogi ya yi tsanani sosai, lamarin da ya jefa dalibai da iyaye cikin firgici, inda iyaye suka garzaya makarantar da zarar suka ji labarin.
‘Yan sanda sun tsaurara tsaro a wajen makarantar, yayin da motocin agajin gaggawa suka cika yankin.
Hukumomin tsaro sun ce ofishin mai gabatar da kara ya fara bincike nan take kan lamarin.
Wannan harin na zuwa ne kwana daya bayan wani harin makamancin haka a Turkiyya, inda wani tsohon dalibi ya ji wa mutane 16 rauni kafin daga bisani ya kashe kansa.
