Fitaccen ɗan kasuwa kuma mai sana’ar fashion a Najeriya, Oluwaseyi Adekunle (Seyi Vodi), ya bayyana yadda ya fara tafiyar kasuwancinsa har ya kai matsayin da yake a yanzu a fannin sutura.
Seyi Vodi, wanda shi ne wanda ya kafa kamfanin Vodi Group, ya ce kudin farko da ya fara samu a rayuwa ya fito ne daga aikin NYSC, wanda ya kai Naira 3,600 kacal.
Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da aka gudanar, inda ya ce wannan kuɗi ya zama ginshiƙin fara tunanin kasuwancinsa.
A cewarsa, a wancan lokaci ya zaɓi ya riƙa adana da saka kuɗin a kasuwanci maimakon kashe su kamar sauran masu hidimar ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa a yau yana samun har zuwa $300,000 domin yin dinki guda ɗaya, yana mai nuna irin ci gaban da kasuwancinsa ya samu a fannin fashion.
Seyi Vodi ya shahara a Najeriya wajen kera tufafi masu inganci, kuma ya samu gagarumar karɓuwa daga manyan mutane a ciki da wajen ƙasar.
