Wani ɗan kasuwa kuma mai ayyukan jin kai, Azeez Yusuf, wanda aka fi sani da Nino Agege, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Agege 02 a Majalisar Dokokin Jihar Legas.
Yusuf yana neman tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin shiga tseren zaben.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a filin Power Line Praying Ground, Orile-Agege, bayan wani shirin tallafin lafiya da ya shirya a yankin.
A cewarsa, burinsa ba na son kai ba ne, sai dai na wakiltar muradin al’umma da kawo ci gaban yankin Agege ta hanyar majalisa.
Ya ce zai ci gaba da ayyukan agaji da yake yi ga marasa galihu, ko da ya samu nasarar lashe zaben, tare da ƙara faɗaɗa su.
Wasu daga cikin jama’a da suka halarci taron sun bayyana goyon bayansu, suna mai cewa Yusuf ya shafe shekaru yana tallafa wa al’umma ba tare da amfani da kuɗin gwamnati ba.
