Shahararren mai wa’azi, Apostle Joshua Selman, ya bayar da tallafin kudi da kayan abinci da suka kai sama da Naira miliyan 200 ga wadanda rikicin Plateau ya shafa.
Ya kai ziyarar ta’aziyya ne zuwa gidan gwamnatin jihar Plateau da ke Jos, inda Gwamna Caleb Mutfwang ya karbe shi tare da jaddada bukatar hadin kai wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya bayyana godiya ga zuwan limamin, yana mai cewa hakan ya nuna goyon baya ga gwamnati da al’ummar jihar a lokacin kunci.
A cewarsa, gwamnati ta tallafa wa iyalan Musulmi da Kiristoci da abin ya shafa domin tabbatar da hadin kai a tsakanin al’umma.
A nasa bangaren, Apostle Selman ya ce ziyarar tasa ta nufin nuna tausayawa da karfafa gwiwar wadanda abin ya shafa.
Ya kuma bayar da kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa kusan 3,000 da sauran kayan agaji, tare da kudi domin tallafa wa iyalan wadanda rikicin ya shafa.
