Wani likita, Dr. Jonah Agwu, ya yi gargadi kan karuwar cutar koda, inda ya ce rashin shan isasshen ruwa da yawan amfani da magungunan rage ciwo na daga cikin manyan dalilai.
Ya bayyana haka ne a wani taro da ƙungiyar National Association of Seadogs (Pyrates Confraternity), Saratoga X Deck, Festac, Lagos ta shirya domin bikin Ranar Lafiya ta Duniya.
Taron ya gudana a Holy Family Health Centre, Festac, Lagos, inda mata masu juna biyu da sauran jama’a suka halarta.
Dalilan cutar koda
Dr. Agwu ya ce cutar koda na ƙaruwa saboda:
Hawan jini da ba a kula da shi
Ciwon suga da ba a kula da shi
Yawan shan magungunan ciwo kamar ibuprofen da diclofenac
Yawan amfani da magungunan gargajiya (agbo)
Rashin shan isasshen ruwa
Ya ce mutane da yawa ba sa shan ko lita ɗaya na ruwa a rana, alhali ya kamata a sha tsakanin lita 2.5 zuwa 3.
Gargadi kan dialysis
Likitan ya ce yin wankin koda (dialysis) yana matakin ƙarshe na cutar koda, kuma ba ya bada tabbacin warkewa 100%.
Gargaɗi kan magungunan gargajiya da labaran ƙarya
Ya gargadi mutane kada su dogara da:
Zobo ko dongoyaro wajen maganin suga
Cewar gishiri ko magani na gargajiya na warkar da cuta
Cewar maganin rigakafi na warkar da jaundice
Shawara ga mata masu juna biyu
Ya shawarci mata masu ciki da su rika zuwa asibiti akai-akai, kuma su karɓi shawarwarin likitoci musamman idan an ba su shawarar haihuwa ta tiyata (CS).
