Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, Gen. Olufemi Oluyede, ya ce shirin Operation Safe Corridor ba lada ga tashin hankali ba ne, sai dai wata dabara ta rage tsattsauran ra’ayi da kawo zaman lafiya mai dorewa a ƙasa.
Ya bayyana haka ne a Gombe, inda ya ce an tsara shirin ne domin magance tushen rikici, tare da taimakawa wajen gyara tunani da sake shigar da wadanda suka yi watsi da tashin hankali cikin al’umma.
Oluyede, wanda Rear Admiral Kabiru Tanimu ya wakilta, ya ce duk da muhimmancin amfani da ƙarfin soja wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, zaman lafiya na gaskiya zai samu ne ta hanyar gyara tunani da sake gina rayuwar mutane.
Ya ce, “Wannan ba lada ba ne, sai dai wata dabarar rage tashin hankali, raunana daukar sabbin ‘yan ta’adda, da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.”
Ya kuma gargadi wadanda suka kammala shirin da su guji komawa tashin hankali, yana mai cewa gwamnati ta ba su damar sake fara rayuwa ne cikin salama da amfani ga al’umma.
Daraktan shirin Operation Safe Corridor, Brig. Gen. Yusuf Ali, ya ce an kafa shirin ne a matsayin hanyar da ta haɗa tsaro da gyara rayuwa, inda mahalarta suka samu horo a fannoni kamar sana’o’i, ilimi, gyaran tunani, da tarbiyya.
Ya ce da dama daga cikin su an tilasta musu shiga rikici ko an yaudare su, kuma yanzu suna da damar sake gina rayuwarsu.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Yahaya, wanda aka wakilta, ya buƙaci wadanda suka kammala shirin da su zama ‘yan kasa nagari, masu bin doka da oda, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa.
An bayyana cewa jimillar mutane 744 ne suka kammala shirin, wanda ke nuna ci gaba da kokarin Najeriya na haɗa matakan soja da na gyaran tunani wajen magance matsalar tsaro a Arewa maso Gabas.
