Hukumar Corporate Affairs Commission (CAC) ta tabbatar da samun kutse a wasu sassan tsarin ta na kwamfuta, lamarin da ya haifar da fara cikakken bincike kan tsaro da tsarin bayanan ta.
A cikin wata sanarwa mai taken “Notice of System Review”, hukumar ta bayyana cewa lamarin ya shafi wasu “ƙananan sassa” na tsarin ta na dijital, inda ta ce an ɗauki matakan gaggawa na dakile matsalar da zarar aka gano ta.
CAC ta ce ta kunna tsarin gaggawa na tunkarar irin wannan hari, tare da fara bincike tare da haɗin gwiwar National Information Technology Development Agency (NITDA) da sauran hukumomin gwamnati da masu fasaha domin gano girman matsalar da tasirinta.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an riga an ɗauki matakan kariya don hana sake samun shiga ba bisa ka’ida ba, yayin da ake ci gaba da binciken fasaha (forensic review).
A matsayin matakin kariya, CAC ta shawarci duk masu amfani da tsarin ta a fadin ƙasa da su kasance cikin kulawa, su duba bayanansu a portal na hukumar, su sabunta kalmomin sirri (passwords), tare da gujewa sakonnin bogi ko na yaudara.
Hukumar ta ce, “CAC na ci gaba da jajircewa wajen kare tsaron bayanan rajistar kamfanoni a Najeriya, kuma za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon cigaba.”
CAC, wadda ke da alhakin rajistar kamfanoni da bayanan kasuwanci a Najeriya, tana ɗaya daga cikin manyan cibiyoyi da ke riƙe da muhimman bayanan kasuwanci na ƙasa, lamarin da ya sa take yawan fuskantar barazanar kutse ta yanar gizo.
Duk da cewa hukumar ta ce matsalar ba ta shafi duka tsarin ba, masana sun yi gargadin cewa irin wannan hari na iya haifar da barazanar satar bayanai da amfani da su ba bisa ka’ida ba.
