Kwamishinan ‘Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), Ahmed Muhammed Sanusi, ya gudanar da rangadi a cibiyoyin rubuta jarabawar kwamfuta (CBT) daban-daban a Abuja, yayin da dalibai suka fara rubuta jarabawar UTME 2026 da hukumar JAMB ke shirya wa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta FCT, SP Josephine Adeh, ta sanyawa hannu, wadda aka wallafa a shafin Facebook na hukuma.
Rangadin, wanda aka gudanar a ranar 16 ga Afrilu, na daga cikin matakan tabbatar da cewa jarabawar za ta gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba, kuma za ta ci gaba har zuwa ranar 18 ga Afrilu, 2026.
A yayin ziyarar, kwamishinan ‘yan sandan ya duba matakan tsaro da aka tanada a cibiyoyin, inda ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun tashi tsaye domin kare dalibai, masu kula da jarabawa, da kuma kayan aiki.
Ya kuma gana da masu kula da cibiyoyin, inda ya tabbatar musu da cikakken kariya daga rundunar ‘yan sanda a duk tsawon lokacin jarabawar.
Sanusi ya kuma gargadi cewa duk wani yunƙuri na tada hankali ko kawo cikas ga gudanar da jarabawar zai fuskanci matakin doka cikin gaggawa.
Ya kara da cewa tura jami’an tsaro da aka yi na da nufin hana duk wani hari ko rikici, tare da tabbatar da cewa dalibai na rubuta jarabawarsu cikin natsuwa ba tare da tsoro ba.
