Fiye da dalibai miliyan 2.2 ne ake sa ran za su rubuta jarabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) ta shekarar 2026 a fadin Najeriya.
Jarabawar, wadda Hukumar Shiga Jami’o’i ta Kasa (JAMB) ke shirya wa, ta fara ne a ranar Alhamis, 16 ga Afrilu, kuma za ta gudana har zuwa ranar 22 ga Afrilu a cibiyoyin da aka tantance a fadin kasar.
Mai rajistar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bukaci jami’an gudanar da jarabawar da su nuna kwarewa da jajircewa, yana mai cewa nasarar wannan aiki na dogara sosai da yadda suka gudanar da aikinsu.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron yanar gizo da aka yi da jami’an fasaha kafin fara jarabawar.
Oloyede ya yaba wa ma’aikata da masu ba da sabis bisa gudunmawar da suka bayar a lokacin gwajin (mock exam), amma ya lura cewa yawancin matsalolin da aka samu sun samo asali ne daga rashin cikakken tantance cibiyoyin jarabawa.
Haka kuma, ya ce za a bayar da kyaututtuka da karin lada ga kungiyoyin da suka nuna bajinta, musamman wajen isar da kayan jarabawa da kuma gabatar da rahotanni cikin lokaci.
Ya kuma sake jaddada cewa hukumar ba za ta lamunci magudin jarabawa ba, tare da gargadin dalibai da kada su shigo da haramtattun kayayyaki cikin dakin jarabawa
