Tsohon mai tsaron raga na Arsenal, Alex Manninger, ya rasu a wani hatsarin mota yana da shekaru 48.
An bayyana cewa kulob ɗinsa na farko, Red Bull Salzburg, ne ya tabbatar da rasuwar tasa a wata sanarwa da ya fitar, inda ya nuna alhini tare da ta’aziyya ga iyalansa da masoyansa.
Manninger ya taka leda a Arsenal tsakanin shekarar 1997 zuwa 2002, inda ya taimaka wa kulob ɗin lashe Premier League da FA Cup a kakar 1997/1998 a karkashin koci Arsène Wenger.
A lokacin da yake Arsenal, ya buga wasanni 64, kuma ya kasance mai taimaka wa fitaccen mai tsaron raga David Seaman, yana kuma da muhimmiyar gudunmawa a wasannin da suka hada da ceton bugun fanareti a gasar FA Cup.
Bayan Arsenal, ya kuma buga wa kungiyoyi daban-daban a kasashen Turai ciki har da Juventus, Augsburg da Espanyol, kafin ya kammala aikinsa a Liverpool ba tare da buga wasa ba.
Rasuwar tasa ta janyo alhini a fadin duniya, musamman a bangaren kwallon kafa, inda magoya baya da tsofaffin abokan wasansa ke ci gaba da bayyana ta’azpiyya.
