Shugaban bangaren horas da masu horarwa a Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Dr. Terry Eguaoje, ya samu sabon lasisi daga US Soccer Federation wanda ke ba shi damar koyar da kwas din B-License.
Wannan nasara na daga cikin kokarin da Eguaoje ke yi na inganta tsarin horas da masu horar da ‘yan wasa a Najeriya.
Tun bayan shigarsa NFF, ya jagoranci shirye-shiryen horaswa daban-daban, ciki har da shirya kwasa-kwasan CAF, da kuma kafa kwas na farko na mata kaɗai a matakin CAF C da B a ƙasar.
Haka kuma, ana sa ran Najeriya za ta dawo cikin tsarin CAF Convention A, wanda zai ba ta damar karbar bakuncin kwas din A-License nan ba da jimawa ba.
Eguaoje ya gode da goyon bayan da yake samu, yana mai cewa wannan sabon mataki ƙarin ƙalubale ne na yin aiki tukuru domin ɗaga martabar masu horar da ‘yan wasa na Najeriya a duniya.
Ya na daga cikin masu horarwa da ke da manyan lasisi daban-daban, ciki har da UEFA A, UEFA B, US Soccer A, da kuma sauran takardun kwarewa a bangaren koyar da ƙwallon kafa.
