Hukumar Kwastam ta Najeriya (Nigeria Customs Service) ta jaddada aniyarta ta ƙara ƙarfafa tsaron iyakoki tare da zurfafa haɗin gwiwar kasuwanci da ƙasar China domin bunƙasa cinikayya ta halal da kuma dakile haramtattun ayyukan kasuwanci.
Kwanturola-Janar na hukumar, Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ganawarsa da jakadan Najeriya da aka tura zuwa China, Abdulrahman Dambazau, a hedikwatar hukumar.
Adeniyi ya ce China ita ce babbar abokiyar kasuwancin Najeriya, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan inganta dangantakar kasuwanci, haɗin gwiwar hukumomin kwastam, da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce hukumar na ƙara tsaurara matakan sintiri a iyakoki domin hana safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba, fasa kwauri, da sauran laifukan tattalin arziki da ke cutar da ƙasa.
Haka kuma ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Kwastam ta Najeriya da Hukumar Kwastam ta China (GACC) domin musayar bayanan sirri da kuma inganta tafiyar da kasuwanci cikin tsari.
A nasa ɓangaren, jakadan ya yaba da rawar da Kwastam ke takawa wajen inganta kasuwanci, yana mai cewa dole ne a ƙara hanzarta shigar da kaya, inganta takardun shaida, da kuma ƙarfafa bin ƙa’idojin shigo da kaya.
Dukkan ɓangarorin sun amince cewa haɗin gwiwa mai ƙarfi zai taimaka wajen ƙara inganta dangantakar kasuwanci tsakanin Najeriya da China tare da rage cin hanci da rashawa a iyakoki.
