Hukumar Nigeria Social Insurance Trust Fund (NSITF) ta bayyana cewa ta yi wa sama da ma’aikata miliyan 7.6 rajista cikin tsarin Employees’ Compensation Scheme (ECS), tare da samun nasarar shigar da rundunar ‘yan sandan Najeriya cikin shirin a matsayin wani babban tarihi.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar NSITF, Oluwaseun Faleye, ne ya bayyana hakan yayin taron 2026 International Civil Service Conference da aka gudanar a Abuja.
Faleye ya ce shigar da rundunar ‘yan sanda cikin tsarin ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, yana mai cewa hakan zai inganta jin dadin jami’ai, kwarin gwiwa da kuma yadda suke gudanar da aikinsu a fadin kasar nan.
A cewarsa, tabbatar da cewa jami’an tsaro da iyalansu sun samu kariya idan suka samu rauni ko suka rasa rayukansu yayin aiki zai taimaka wajen kara karfin tsaro a Najeriya.
“Mun yi wa sama da ma’aikata miliyan 7.6 rajista cikin tsarin. Mun kuma samu nasarar shigar da rundunar ‘yan sandan Najeriya cikin ECS bayan ganawa da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda,” in ji shi.
Ya kara da cewa idan jami’an tsaro sun san cewa iyalansu za su samu kariya idan wani abu ya same su yayin aiki, hakan zai kara musu kwarin gwiwa da jajircewa.
