Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa, JAMB, ta saki sakamakon dalibai 279 na jarabawar UTME ta shekarar 2026 da aka dakatar tun farko saboda zargin magudin jarabawa.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis ta cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, inda ya ce sakin sakamakon na daga cikin ci gaba da tantance batutuwan da aka yi wa alama yayin gudanar da jarabawar.
Benjamin ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan cikakken bincike kan daliban da aka rike sakamakonsu a lokacin gudanar da jarabawar.
A cewarsa, yayin da aka soke sakamakon wasu dalibai bayan tabbatar da aikata magudi, an saki na wasu bayan hukumar ta tabbatar babu wata hujja da ke nuna sun aikata laifi.
“An soke wasu sakamako kai tsaye inda aka tabbatar da magudi, yayin da aka saki wasu bayan hukumar ta gano babu wata hujja ta farko da ke nuna suna da hannu a laifin,” in ji shi.
Ya kara da cewa sakamakon cibiyoyin jarabawa da tsarin sa ido na JAMB ya yi wa alama saboda wasu abubuwan da ake zargi ko kuma wadanda aka samu rahotanni marasa kyau a kansu, za su ci gaba da kasancewa a rike har sai an kammala bincike.
Benjamin ya ce duk wani dalibi da aka samu da laifi bayan binciken za a soke sakamakonsa.
An gudanar da jarabawar UTME ta shekarar 2026 tsakanin ranar 16 zuwa 25 ga watan Afrilu a cibiyoyin CBT da aka amince da su a fadin kasar nan.
