Fitacciyar jarumar Nollywood mai lashe kyaututtuka, Kehinde Bankole, ta yi kira kai tsaye ga Gwamnatin Tarayya, Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, da kuma hukumomin leken asiri na kasar nan da su gaggauta daukar matakan murkushe yawaitar satar mutane a Najeriya.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Laraba, jarumar ta bayyana cewa ‘yan Najeriya sun gaji da jin sakonnin ta’aziyya kawai, suna bukatar ganin matakan aiki na gaskiya domin ceton rayuka.
Ta ce: “Ba batun dalilin da yasa hakan ke faruwa ba ne yanzu, rayuka ake rasa wa! Wannan bai kamata ya zama sabon al’ada ba a 2026 inda yara ke gudu don ceton rayukansu.”
Bankole ta kuma yi martani kan rade-radin cewa ana amfani da matsalar satar mutane wajen bata sunan gwamnati, tana mai cewa ko da hakan gaskiya ne, ya kamata hakan ya kara zaburar da hukumomin tsaro wajen yin aiki mai tsauri.
Ta ce hukumomi su hada kai su tilasta aiki ga DSS, NIA, Ma’aikatar Tsaro da sauran hukumomi domin gano masu aikata laifin da kawo karshen matsalar.
Jarumar ta kara jaddada cewa lokaci ya yi da shugabanni za su daina dogaro da maganganun ta’aziyya kawai, su mayar da hankali kan daukar matakin da zai kawo sakamako.
Kalaman nata na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar fargaba a kasar nan sakamakon yawaitar sace-sacen mutane, ciki har da sace dalibai da malamai a Ogbomoso, jihar Oyo.
