Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyarar girmamawa ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso, a daren ranar Talata.
Shugabannin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) sun gana ne jim kadan bayan kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya tantance tare da amincewa da Peter Obi domin shiga zaben fidda gwani na shekarar 2027.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, Kwankwaso ya tabbatar da ganawar da aka yi a gidansa da ke Maitama, Abuja.
Kwankwaso ya bayyana Obi a matsayin “dan uwana” tare da nuna kwarin gwiwa kan makomar jam’iyyar.
“Jiya da daddare na karbi bakuncin dan uwana, Mai Girma Peter Obi, bayan nasarar da ya samu a tantancewar ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu ta NDC. Makomar gaba tana da haske kuma cike take da alkawari,” in ji Kwankwaso.
Ziyarar na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Obi da Kwankwaso suka shiga jam’iyyar NDC a farkon watan Mayun 2026 bayan ficewarsu daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Masu sharhi kan siyasa na ganin wannan sauyi a matsayin wani babban hadin gwiwa tsakanin jagororin adawa gabanin zaben 2027, musamman yayin da ake rade-radin cewa za su iya tsayawa takara tare a karkashin tikitin hadaka.
A ranar Talata, kwamitin tantancewar NDC ya amince da Obi ba tare da hamayya ba, bayan rahotanni sun nuna cewa shi kadai ne ya sayi fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Rahotanni sun kuma nuna cewa shugabannin biyu na ci gaba da tattaunawa kan yadda za a karfafa bangaren adawa domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zab9en 2027.
