Reshen jihar Nasarawa na jam’iyyar Labour Party da ke biyayya ga bangaren Julius Abure ya fara rabon fom ɗin neman takara (expression of interest da nomination forms) kyauta ga ‘ya’yan jam’iyya da masu sha’awar takara a jihar.
An gudanar da rabon fom ɗin ne a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia, inda ya shafi kujerun gwamna, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da kuma ‘yan majalisar dokokin jiha.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Alexander Ombugu, ya ce matakin bayar da fom kyauta an dauke shi ne domin rage nauyin kudi ga masu neman takara sakamakon matsin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar.
Ya bayyana cewa an tsara gudanar da zabukan fidda gwani tsakanin 27 zuwa 29 ga Mayu, 2026, inda za a yi na gwamna da majalisar dokoki a ranar 27, sannan na sanatoci da wakilai a ranar 29.
Haka kuma ya ce za a gudanar da zabukan fidda gwani na cike gurbin Sanatan Nasarawa ta Arewa a ranar 25 ga Mayu, gabanin zaben da hukumar Independent National Electoral Commission (INEC) ta shirya.
Ombugu ya bukaci ‘yan siyasa masu gaskiya da kwarewa su fito su nemi takara, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar za ta gudanar da zabe cikin gaskiya da zaman lafiya duk da rikicin shugabanci da ke ci gaba a cikinta.
Jam’iyyar Labour Party dai tana ci gaba da fuskantar rabuwar kai tsakanin bangaren Julius Abure da kuma bangaren da ke goyon bayan Senata Nenadi Usman, amma duk da haka bangarorin biyu na ci gaba da shirye-shiryen zaben 2027.
