Kocin Ingila, Thomas Tuchel, ya ce ba shi da wata fargaba duk da ya cire wasu manyan ‘yan wasa masu hazaka daga cikin jerin ‘yan wasan da zai kai Gasar Kofin Duniya.
Tuchel ya ce manufarsa ita ce gina tawaga mai ƙarfi da daidaito, ba wai kawai tara fitattun ‘yan wasa mafi hazaka ba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a Wembley, inda ya ce a shirye yake ya tafi da ‘yan wasa 26 da zai yi imanin za su iya taimaka masa lashe gasar.
Kocin ya yanke shawarar barin wasu manyan ‘yan wasa kamar Phil Foden, Cole Palmer da Trent Alexander-Arnold, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.
Haka kuma an cire wasu kamar Harry Maguire, Luke Shaw da Morgan Gibbs-White, yayin da Ivan Toney mai taka leda a Saudi Arabia ya samu gurbi a cikin tawagar.
Tuchel ya ce, “Tawaga ce ke lashe gasa, ba kawai sunayen ‘yan wasa ba.”
Ya kara da cewa dole ne koci ya yi zaɓi mai wahala domin samun daidaito a cikin tawaga, tare da burin lashe Kofin Duniya.
