Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Enugu ta tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane da fashi da makami da ke addabar al’ummomin kan iyaka tsakanin jihohin Enugu da Benue.
Wadanda aka kama sun hada da Mohammed Hassan, mai shekara 28, da Aminu Usman, mai shekara 26, dukkaninsu ‘yan asalin Otukpa a ƙaramar hukumar Ogbadibo ta Jihar Benue.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, SP Daniel Ndukwe, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce an kama su ne a ranar 14 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 1:20 na rana a Amutenyi, Obollo-Afor, a ƙaramar hukumar Udenu ta Jihar Enugu, ta hannun jami’an sashen ‘yan sanda na Udenu tare da haɗin gwiwar ‘yan sa-kai (Neighbourhood Watch).
An bayyana cewa an samu nasarar kama su ne bayan bayanan sirri da aka tattara kan motsin ƙungiyar da ake zargin tana aikata laifuka a yankin.
Sanarwar ta ƙara da cewa an gano bindiga kirar Beretta guda ɗaya mai harsashi biyu na 9mm, babura uku da ake zargin an sace, waya guda, wasu layu da ake zargi, katin ATM, makullai da kuma kuɗi N4,700 a hannunsu.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin na cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke satar babura tare da aikata fashi a yankunan da ke kan iyaka tsakanin Enugu da Benue.
Rundunar ‘yan sandan ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Giwa, ya yaba da aikin jami’an, yana mai cewa rundunar ba za ta huta ba har sai an kawar da miyagun mutane daga jihar.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.
