Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka (ICPC) ta musanta zargin cewa tsare tare da gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na da nasaba da siyasa, tana mai cewa tana gudanar da aikinta ne bisa doka da kundin tsarin hukuma.
Hukumar ta kuma karyata ikirarin cewa an hana El-Rufai samun kulawar lafiya ko abinci a lokacin da yake tsare, inda ta ce yana da damar ganin likitocin da ya zaba tare da karɓar ziyartar ‘yan uwansa cikin lokutan da aka amince da su.
Mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce El-Rufai yana nan a tsare ne saboda bai cika sharuɗɗan beli da kotu ta gindaya masa ba.
Ya ce: “Kotu ta ba shi beli amma har yanzu bai cika sharuddan ba. Idan ya cika su, za mu sake shi nan take. Ba mu riƙe shi ba ne bisa son rai.”
ICPC ta ce shari’ar da ake yi masa tana gaban kotu ne, don haka bai kamata a haɗa ta da siyasa ba.
Hukumar ta ce El-Rufai yana samun kulawa ta lafiya, kuma an kai shi asibitin likitan haƙora da na ido sau biyu a makon da ya gabata.
Haka kuma ta ƙara da cewa yana samun ziyara daga ‘yan uwansa, ciki har da matarsa da mai aiki a gida, a lokuta da dama da suka dace da dokar hukumar.
ICPC ta bayyana cewa dukkan matakan tsaro da take ɗauka na da nufin kare shi da sauran waɗanda ke tsare, musamman saboda matsayin sa na tsohon gwamna.
Ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa ana amfani da batun ne don siyasa, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da bin doka ba tare da tsoma siyasa a cikin aikinta ba.
