Hedikwatar Tsaro ta kasa (Defence Headquarters – DHQ) ta fara shari’ar wasu jami’an soji sama da 30 da ake zargi da kitsa yunkurin kifar da gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu.
An fara sauraron karar ne a ranar Juma’a, 24 ga Afrilu, 2026, a wani wuri na musamman da ake kira Scorpion Mess, inda aka hana ‘yan jarida shiga domin daukar rahoto.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake tuhuma sun isa wurin shari’ar da misalin karfe 8:54 na safe cikin motar rundunar soji ta Army Headquarters Garrison, sannan wata motar sashen leken asiri na soji (DIA) ta biyo baya.
Tun da farko, DHQ ta bayyana cewa za a gurfanar da dukkan jami’an da ake zargi a gaban kotun soja (court martial) bayan kama su da aka yi a watan Oktoban shekarar 2025 da kuma kammala bincike a kansu.
A wani bangare kuma, an riga an gurfanar da wasu mutane shida fararen hula da kuma tsofaffin jami’an soja a gaban kotun tarayya da ke birnin Abuja, inda daga bisani aka tsare su a hannun Hukumar DSS.
