Shugaban kuma wanda ya kafa cocin Living Faith Church Worldwide, Bishop David Oyedepo, ya bukaci mabiyansa da su rika ba masu garkuwa da mutane lambar wayarsa idan aka sace su.
Ya ce yana da ikon ruhaniya da zai iya taimakawa wajen tabbatar da sakin duk wanda aka yi garkuwa da shi daga cikin mambobin cocinsa.
Oyedepo ya bayyana hakan ne yayin wa’azi a cocin Canaanland da ke Ota, hedikwatar cocinsa.
Wani faifan bidiyo na wa’azin ya karade kafafen sada zumunta a ranar Alhamis, inda aka ga kalamansa na jawo cece-kuce.
“Idan wani ya kama ku, ku ba su lambar wayata,” in ji shi.
Ya kara da cewa akwai lokuta biyu da ya ce an samu “ceton allahntaka” ga mambobin cocinsa da aka sace.
A cewarsa, a wani lamari, an sace wani fasto na cocin, inda aka ba shi wayar wanda ya yi garkuwar, sannan ya yi barazanar cewa idan ba a saki mutumin ba cikin awanni 24, zai mutu.
Ya kuma ce a wani lamari daban, wata mamba ta cocin ta ce za ta fito daga hannun masu garkuwa da ita kafin karfe 7 na safe, kuma daga karshe an sake ta ba tare da kiran sa ba, inda ya ce masu garkuwar sun fara cutar kansu kafin sakin ta.
Oyedepo ya jaddada cewa mambobin cocinsa suna dauke da “ikon ruhaniya” da ya ce ya fi karfin mugunta, yana mai cewa dole ne su gane su yi amfani da wannan iko.
Bidiyon, wanda aka wallafa da taken #SupersonicSunday a shafukan cocin, an ce an dauke shi ne a wani taro kafin ya fara yaduwa sosai a kafafen sada zumunta.
