Sanata mai wakiltar Delta North, Ned Nwoko, ya yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki a yankin Kudu maso Gabas da su hada kai wajen goyon bayan kirkirar Jihar Anioma a matsayin sabuwar jiha ta shida a yankin.
Nwoko ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce lokaci ya yi da dukkan masu fafutukar neman jihohi daban-daban a Kudu maso Gabas su hade karfi su mayar da hankali kan Anioma a matsayin wata dama ta tarihi.
Ya ce hadin kai zai taimaka wajen cimma muradin cigaban tattalin arziki da daidaito a cikin tsarin raba jihohi a Najeriya.
Wannan kira na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan batun kirkirar jihar Anioma a matakin kasa. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya taba bayyana goyon baya ga matakin, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar aiwatar da shi.
Nwoko ya ce idan aka kirkiri Anioma, zai taimaka wajen bude kofar kasuwancin ruwa, bunkasa harkokin sufuri, da kuma jawo zuba jari a fannoni kamar noma, man fetur da gas, da kuma harkokin jiragen ruwa.
Ya kuma bayyana cewa hakan zai taimaka wajen hade al’ummomi masu alaka da juna a yankunan Delta, Kudu maso Gabas da wasu sassan Edo, wanda zai kara karfafa hadin kan kasa.
A cewarsa, akwai bukatar masu fafutuka su guji rarrabuwar kai, su maida hankali kan manufofi masu amfani da za su kawo ci gaba ga yankin gaba daya.
