Shahararriyar mawakiya kuma ‘yar Mavin Records, Ayra Starr, ta bayyana cewa ta guji yin soyayya tun tana makaranta domin kare mutuncinta da hotonta a gaba.
Ayra Starr, mai shekaru 23, ta bayyana hakan ne a wata hira da Quenlin Blackwell, inda ta ce ba ta son daga baya a ce ita tsohuwar budurwar wani ce bayan ta zama shahararriya.
Ta ce ta kasance mai lura da kanta sosai, tana kuma shakku kan dalilin da yasa wasu maza ke nuna mata sha’awa a wancan lokacin.
“Ban shiga soyayya a makaranta ba saboda ban so daga baya a ce ni tsohuwar budurwa ce ta wani. Na lura cewa da dama suna zuwa ne da wani buri a zuciya,” in ji ta.
Ayra Starr ta kuma ce a yanzu tana da wasu ka’idoji a zaɓin abokin zama, inda ta bayyana cewa ilimi da hankali sun fi muhimmanci a gare ta fiye da kyawu.
Maganganunta sun jawo tattaunawa a kafafen sada zumunta, inda magoya baya ke yaba mata kan tsantsar hangen nesa da ta nuna tun tana ƙuruciya.
