Tsohon Babban Daraktan Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana cewa sammacin kama da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Asusun Jama’a ya bayar a kansa ya ba shi mamaki matuka, yana mai cewa bai ki amsa gayyatar kwamitin ba kamar yadda ake zargi.
Kyari ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban kwamitin, bayan da majalisar ta bayar da umarnin kama shi sakamakon rashin bayyana a wani zaman bincike da ake gudanarwa kan harkokin kudaden Kamfanin NNPCL.
A cewarsa, tun kafin zaman ya gudana ya sanar da kwamitin cewa yana kasar waje domin samun kulawar lafiya, kuma ya bayyana shirinsa na halartar zaman da zarar ya dawo Najeriya.
“Ina nan a shirye kuma ina da cikakken niyyar mutunta gayyatar kwamitin da bayyana a gabansa da zarar na dawo Najeriya,” in ji Kyari.
Ya musanta zargin cewa ya yi watsi da gayyatar majalisar, yana mai cewa bai samu wata sabuwar sanarwa ko gayyata daga kwamitin ba kafin a bayar da sammacin kama shi.
“Da a ce gayyatar ta same ni, da babu wata-wata zan halarta domin ba ni da abin da nake boyewa,” ya bayyana.
Kyari ya ce halin lafiyarsa a yanzu ba ya ba shi damar komawa gida domin amsa tambayoyin kwamitin, inda ya bukaci a rika tuntubar lauyoyinsa idan akwai wani muhimmin sako yayin da yake ci gaba da jinya.
Tsohon shugaban NNPCL din ya kuma kare aikinsa a lokacin da yake jagorantar kamfanin, yana mai cewa ya taimaka wajen sauya NNPCL daga kamfani mai asara zuwa wanda ke gudanar da harkokinsa bisa tsarin kasuwanci mai anfani.
Ya kara da cewa dukkan mu’amalolin da aka gudanar a lokacin mulkinsa suna da cikakkun bayanai kuma a bude suke ga duk wani bincike na doka.
A halin yanzu dai, Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Asusun Jama’a na gudanar da bincike kan wasu bayanan kudade da mu’amalolin NNPCL da ake cewa darajarsu ta haura naira tiriliyan N210.
An bayar da sammacin kama Kyari ne bayan kudirin da Sanata Victor Umeh ya gabatar, tare da goyon bayan Sanata Adams Oshiomhole, bayan ya kasa halartar zaman kwamitin.
Sai dai Kyari ya jaddada cewa yana da niyyar hada kai da binciken majalisar gaba daya, kuma zai bayyana a gaban kwamitin da zarar likitoci sun tabbatar ya samu sauki.
