Fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya, Dayo Amusa, ta soki abin da ta bayyana a matsayin matsin lamba da cin zarafi da ake yi wa fitattun mutane da masu sana’ar nishaɗi a kafafen sada zumunta kan batutuwan da suka shafi ƙasa.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce mutane da dama a masana’antar nishaɗi na fuskantar suka da hare-hare a yanar gizo.
A cewarta, ana suka musu idan sun bayyana ra’ayinsu, sannan kuma ana zarginsu da rashin tausayi idan suka ci gaba da gudanar da ayyukansu yayin da ake fuskantar wasu matsaloli a ƙasa.
Amusa ta ce masu shirya fina-finai kan karɓi rance daga bankuna da kuɗin ruwa mai tsada domin samar da fina-finai, amma duk da haka wasu na sa ran su dakatar da ayyukansu gaba ɗaya domin su rika wallafa saƙonni kan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasa.
Ta jaddada cewa ba za ta bari masu cin zarafi a kafafen sada zumunta su rinjaye ta ba, tana mai cewa ba ta gina sunanta domin faranta ran masu tada ƙura a yanar gizo ba.
Jarumar ta kuma gargadi masu kai mata hari a shafukanta da su guji yin hakan, tana mai cewa ba za ta lamunci raini ko cin fuska ba.
Duk da fushinta kan lamarin, Amusa ta nuna alhini kan sace ɗalibai da malamai a jihar Oyo, inda ta yi addu’ar Allah ya kubutar da su tare da dawo da su gida lafiya.