Gwamnan jihar Benue, Rabaran Firist Hyacinth Alia, ya musanta rade-radin da ke cewa an cire sunansa daga jerin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC da aka tantance domin shiga zaben fidda gwani da ake gudanarwa yau.
Gwamnan ya bayyana cewa sunansa yana cikin jerin ‘yan takarar da aka tantance kuma babu lokacin da aka cire shi daga cikin jerin.
Alia ya ce kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna na APC karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya tantance tare da amincewa da takararsa.
Da yake mayar da martani kan jita-jitar ta shafinsa na Facebook a safiyar Alhamis, babban mai magana da yawun gwamnan, Sir Tersoo Kula, ya bayyana Alia a matsayin “tauraron dan siyasa,” tare da kira ga magoya bayan APC da su je cibiyoyin kada kuri’a na mazabunsu domin tabbatar da nasarar gwamnan ta hanyar zaben kai tsaye.
A cewar Kula, “Yau rana ce ta Gwamna Alia. Kwamitin da ya tantance gwamnoni masu ci na APC shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya jagoranta.
“Kwamitin da ya tantance sauran ‘yan takara daban yake. Saboda haka, wannan kwamitin ba shi da ikon fitar da jerin kwamitin da ya tantance gwamnoni masu ci.
“Fr. Hyacinth Iormem Alia mutum ne na musamman. A lokacin tantancewar, shugaban jam’iyyar na kasa ya kira shi gwamnan da ya fi so. Yau ce ranar nasara. Mu je mazabunmu domin tabbatar da ci gaba. Da Alia, Benue za ta kara girma,” in ji shi.
Tun da farko dai wasu jerin sunayen ‘yan takarar gwamna na APC da aka tantance sun yadu, inda a wani jerin ba a ga sunan Alia ba, yayin da wani daban ya kunshi sunansa tare da sauran ‘yan takara hudu.
