An kubutar da mataimakiyar shugaban karamar hukumar Ilejemeje ta jihar Ekiti, Misis Grace Ogunleye, daga hannun masu garkuwa da mutane bayan kwanaki kadan da sace ta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Ado Ekiti ranar Alhamis, inda ya ce an ceto jami’ar gwamnatin cikin koshin lafiya ba tare da wata illa ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace Ogunleye ne ranar Laraba a hanyar Ipere zuwa Iludun Ekiti. Daga baya an gano motarta a yashe, yayin da ba a san inda take ba, sannan wayarta ta kasance a kashe.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, “An kubutar da Misis Grace Ogunleye, mataimakiyar shugaban karamar hukumar Ilejemeje, wacce wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace ranar 20 ga Mayu, 2026.”
Ya ce nasarar ceto ta samu ne sakamakon hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda, sojoji, sauran hukumomin tsaro da kuma jami’an tsaron sa-kai da suka gudanar da aikin ceto tare da matsa lamba kan masu garkuwar.
Abutu ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Micheal Falade, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma wadanda ke da hannu a ciki.
A baya dai, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a cocin Christ Apostolic Church da ke Eda Oniyo a karamar hukumar Ilejemeje ranar 28 ga Afrilu, 2026 yayin wani taro, inda suka kashe fasto tare da yin garkuwa da kimanin masu ibada 15.
Har yanzu wadanda aka sace a cocin na hannun masu garkuwa, yayin da hukumomin tsaro suka ce ana ci gaba da kokarin kubutar da su cikin koshin lafiya.
