Matafiya da ke amfani da hanyar Ilorin zuwa Igbeti a Jihar Kwara sun shiga mawuyacin hali bayan ambaliyar ruwa ta mamaye gadar Moro da ta riga ta rushe, lamarin da ya hana zirga-zirga a wannan muhimmiyar hanya.
Ruwan sama mai karfi da aka yi da daddare ne ya haddasa cikar kogin Moro, wanda ya mamaye yankin tare da jefa motoci cikin ruwa yayin da fasinjoji suka makale suna jiran ceto.
Gadar Moro da ke tsakanin Oko-Olowo/Mandala da karamar hukumar Asa ta ruguje tun ranar 30 ga Afrilu bayan wata babbar mota ta bi ta kanta.
Lamarin ya katse muhimmiyar hanyar da ke hada Jihar Kwara da Oyo da sauran yankuna zuwa iyakar Jamhuriyar Benin.
Ambaliyar ruwan da ta biyo baya ta kara dagula al’amura, musamman ganin cewa har yanzu ba a kammala hanyar wucin gadi da gwamnatin jihar ta yi alkawari ba.
Rahotanni daga wurin sun nuna yadda motoci suka nutse a ruwa, yayin da matafiya ke kokarin tsallakewa cikin mawuyacin hali.
Mazauna yankin sun nuna damuwa kan jinkirin gyaran gadar, suna gargadin cewa matsalar na iya kara tsananta yayin da damina ke karatowa.
Wata mazauniyar yankin mai suna Kafayat ta bayyana cewa lamarin ya jawo tsaiko ga harkokin kasuwanci tare da kara kudin sufuri ga jama’a.
Haka kuma, wasu mazauna yankin sun yi tambaya kan dalilin da yasa aikin wata gada ta daban da aka fara a kusa da wurin ya tsaya cik na tsawon shekaru.
Al’ummomin yankin sun bukaci daukar matakin gaggawa domin kaucewa mummunar matsala yayin da ake sa ran karin ruwan sama a watanni masu zuwa.
