Dan wasan Manchester United, Bruno Fernandes, ya shiga sahun manyan ‘yan wasa masu yawan bayar da kwallaye a tarihin gasar Premier League bayan ya kai assists 20 a kakar wasa ta 2025/2026.
Wannan nasara ta sanya Fernandes cikin jerin fitattun masu kirkirar dama a gasar Ingila, tare da daidaita tarihin mafi yawan assists da aka taba yi a kaka guda.
A cewar rahotanni, manyan ‘yan wasan da suka yi fice a wannan bangare sun hada da Cesc Fàbregas, Frank Lampard, Mohamed Salah, Mesut Özil, da kuma Bruno Fernandes.
Fàbregas ya taba yin assists 17 tare da Arsenal a kakar 2007/08, sannan ya kara da 18 a Chelsea a 2014/15.
Frank Lampard ma ya yi assists 18 a kakar 2004/05 lokacin da Chelsea ta lashe gasar karkashin José Mourinho.
Mohamed Salah ya shiga wannan jerin ne bayan ya yi assists 18 a kakar 2024/25 tare da Liverpool.
Mesut Özil kuwa ya yi assists 19 a kakar 2015/16, inda ya nuna bajintarsa a Arsenal.
Bruno Fernandes yanzu ya kai 20 assists, abin da ya tabbatar da muhimmancinsa ga nasarar Manchester United da dawowarta gasar Champions League.
Nasarar tasa na nuna irin tasirin da yake da shi wajen kirkirar dama da jagorantar kungiyar zuwa manyan nasarori.
